Skip to main content

RA'AYI : Murtala Garo Da Maganar Tallafawa Rayuwar Matasa A Kano

 


Daga Ishaq Muttaka Magashi


Ba wani sabon abu ba ne idan a ka sake nanata wa mutane irin tallafawa rayuwar matasa da mata da Kwamishinan Kananan Hukumomi na Jihar Kano, Murtala Sule Garo ke yi a wannan mulkin na Maigirma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje. 


Mu matasa 'yan Kano mazauna jihohin Arewa Ta Tsakiya na Najeriya, baya ga bibiyar ayyukan raya kasa da Kwamishina Murtala Garo yake yi a daukacin kananan hukumomi 44 na Jihar, mun shaida tare da misalai barkatai, na yadda ya yi fice wajen tallafawa rayuwar matasa da masu karamin karfi da kuma marasa aikin yi. 


Ba tare da wani cika baki ba, mu na sanarwa mai karatu cewar, ya je ko ya sa a duba masa a ga yadda ofis din Garo ke cika duk lokacin da a ka ce ya na cikin ofis. Mutane ne kawai daruruwa ke yin tururuwa wajen ganinsa. Daga masu maganar ayyukan al'umma sai masu kai masa bukatun kansu. Hatta a gidansa ma mutane ne ke yin tururuwa. 


Kullum maganar Murtala Garo ita ce mutane, musamman matasa, su tsaya da kafarsu. Ya kan ce musu "A kama sana'a 'yan uwana, zaman banza ba namu ne ba."


Mu fa a wajenmu ba aibu ba ne wai dan Jami'ai sun gayyace shi dan tattauna yadda za a kara samar da zaman lafiya a wannan jiha ta mu. Ganin yadda harkokin siyasa ke kara kankama a wannan jiha ta mu. 


Mai kishin matasa da al'umma shi ke da dabarun sanin yadda za a gyara rayuwar matasan. Wannan ko shakka babu. Mutumin da a ke masa kirari da Kwamandan tabbatar da Adalci da kuma ci gaban jama'a, menene kuma sabo a wajensa a harkar siyasa a yanzu haka?

 

A matsayinmu na 'yan Kano samari mazauna jihohin Arewa Ta Tsakiya na kasar nan, mu na kara jaddada fatan alherinmu ga Murtala Sule Garo da yunkurinsa na ganin an magance zaman banza tsakanin al'umma musamman mata da matasa. Saboda inganta harkar tsaro a wannan kasa ta mu.


Mu na kuma tare da yabon da Gwamnan Kano Ganduje ya yi wa Murtala Garo kwanan baya yayin wani taron wata mashahuriyar kungiyar kawo ci gaban al'ummar mazabar Majalisar Dattijai na Kano Ta Arewa. Wanda a ka yi taron a dakin taro na Africa House a gidan gwamnati. Baba Ganduje mu na godiya.

BA ABINDA ZA MU CE SAI MA RANAR KAWAI !!!


Daga Ishaq Muttaka Magashi

Shugaban Kungiyar Samarin 'Yan Kano Mazauna Jihohin Arewa Ta Tsakiya

IshaqMM@gmail.com

Comments

Popular posts from this blog

Youthful Excellence Personified: The Inspiring Story of Dahir M Hashim

  By Sule Sani Sule In a world where youthful exuberance is often marred by self-interest and fleeting passions, it's refreshing to come across individuals like Dahir M Hashim, the Commissioner for Environment and Climate Change in Kano State. His remarkable story serves as a beacon of hope, reminding us that the youth of today can indeed drive positive change. Hashim's journey is a testament to the power of dedication, hard work, and a genuine commitment to creating a better world. Long before he assumed his current role, he was already making significant contributions to the field of climate change and environmental affairs. His expertise and passion have not gone unnoticed, as evidenced by his appointment as Commissioner by Governor Abba Kabir Yusuf ¹. Under Hashim's leadership, the Ministry of Environment and Climate Change has undergone a remarkable transformation. His efforts have been instrumental in tackling environmental challenges, and his commitment to sustainabi...

Aisha Garba’s Bold Vision for Transforming Basic Education in Nigeria

By Suhaib Auwal   In a country where the foundational pillars of education have long been riddled with structural gaps, funding constraints, and policy inconsistencies, the recent leadership at the Universal Basic Education Commission (UBEC) signals a renewed hope.  Since her appointment as the Executive Secretary of UBEC, Aisha Garba has embarked on a reformist mission that seeks not just to address the surface-level symptoms, but to cure the systemic ailments crippling Nigeria’s basic education sector. At the core of her vision is a comprehensive, inclusive, and technology-driven approach to strengthening basic education delivery. Her leadership style is not only proactive, but it also reflects a deep understanding of Nigeria's complex educational terrain.  With over 17 million children currently out of school, Garba has made it unequivocally clear: this figure is unacceptable, and she intends to drastically reduce it within the shortest possible time. A Three-Pronged V...

DISRESPECTING COURT ORDER REGARDING KANO EMIRATE CRISIS

   By Dr. Usman Suleiman Sarki Law and order are the bedrock of harmonious living in every human society.  This necessitated the establishment of judicial system responsible for the enforcement of law and order as well as the settlement of disputes between parties.  One most important organ of the judiciary is the Court that determines cases brought before it using appropriate legal procedures. In an effort to ensure the proper discharge of its duties, the court gives order(s) to individuals, group, organizations/institutions and state mandating them to refrain or undertake an action before or after judgement. In line with the above, a federal high court sitting in Kano received a petition seeking for its intervention on matters relating Kano Emirate Crisis as the state House of Assembly passed a bill for the dissolution of the Five Emirates in the state where the court gives an order restraining the Kano state Governor from assenting a bill into and implementing the...