Kwamitin amintattu na dan takarar gwamnan jihar Kano Malam Inuwa Waya (Raba Gardama) ya fara rabon tallafin azumi ga shugabannin jam'iyyar APC na kananan hukomumi 44 dake Kano.
Kwamitin karkashin jagorancin Abbas Sunusi Abbas sun fara rabon tallafin ne a yau alhamis daga karamar hukumar birni da kuma Gwale, inda za'a ci gaba har sai an zagaye kananan hukomumi 44 dake fadin jihar Kano.
Da yake jawabi a Kananan hukumomi biyu da aka kai wa tallafin, Shugaban Kwamitin Amintattu na Malam Inuwa Waya dan takarar gwamnan jihar Kano, Alhaji Sunusi Abbas Sunusi ya bayyana cewa " Mun zo ne madadin Malam Inuwa Waya domin isar sakon gaisuwar barka da azumi da kuma bayar da tallafi gare ku a matsayin ku na shugabannin jam'iyya wanda kuke bamu gudunmawa ta musaman."
Ya kara da cewa " Malam Inuwa Waya yana sane da irin ayyukan ci gaban jam'iyya da kuke gudanarwa, a don haka ne ya sanya ku cikin Rukunin mutane na farko da za'a bawa tallafin azumi."
Tallafin da aka bawa shugabannin jam'iyyar ya hada da buhuhunan Shinkafa, Taliya da sauran kayan masarufi.
A gobe juma'a ne Kwamitin zai ci gaba da rabon tallafin, inda za'a kai kananan hukumomin Fagge da Dala.
Comments
Post a Comment