Muƙaddashin yaɗa labarai na Jam'iyyar NNPP na jihar Kano, Honarabil Musa Nuhu Ƴankaba ya yi kira ga Ƴan Adaidaita Sahun jihar Kano da su tabbata sun zaɓi Abba Kabir Yusuf a matsayin Gwamnan jihar Kano a zaɓe mai zuwa domin fitar da su daga ƙangin da Jam'iyyar APC take ƙoƙarin jefa su a jihar Kano. Kiran nasa na zuwa ne kwana ɗaya bayan Gwamnatin jihar Kano ta fitar da dokar hana Ƴan Adaidaita Sahun zirga-zirga a wasu daga cikin manyan titunan jihar Kano. A cewar sa, hana Ƴan Adaidaita Sahun zirga-zirga a manyan titunan Kano daidai yake da hana mutum miliyan ɗaya neman abincin su a jihar Kano. Ya kara da cewa kamata ya yi Gwamnati ta fara sama musu abin yi kafin ta ɗauki wannan mummunan mataki a kan su.
Factual and verifiable Political News