Babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kano kan daukar hoto Aminu Dahiru ya raba kayan abinci ga shugabanni da ‘ya’yan jam’iyyar APC na karamar hukumar Gwale. Shirin rabon ya zo ne kwana guda gabanin Sallah, wanda yana daga cikin manufofinsa na taimaka wa ‘ya’yan jam’iyyar da nufin rage musu radadin rayuwa da aka fuskanta a 'yan kwanakin baya. Da yake jawabi a wurin rabon kayayyakin, Aminu Dahiru, babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kano kan daukar hoto, Aminu Dahiru, ya jaddada kudirinsa na tallafawa ‘ya’yan jam’iyyar APC a dukkan matakai, ta hanyar raba musu kayan tallafi ga dattawan jam’iyyar da kuma bayar da tallafi ga mata da matasa domin su dogara da kansu. Ya kara da cewa yanzu ne daidai lokaci ne da ya dace da shi da sauran wadanda suka amfana da gwamnatin APC su koma gida domin tallafi jama’arsu, wanda hakan zai taimaka masu a siyasar da zasu gudanar a nan gaba. Aminu Dahiru ya yi alkawarin ci gaba da kyautata alakarsa da mutane, ind...
Factual and verifiable Political News