Babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kano kan
daukar hoto Aminu Dahiru ya raba kayan abinci ga shugabanni da ‘ya’yan jam’iyyar
APC na karamar hukumar Gwale.
Shirin rabon ya zo ne kwana guda gabanin Sallah, wanda yana
daga cikin manufofinsa na taimaka wa ‘ya’yan jam’iyyar da nufin rage musu
radadin rayuwa da aka fuskanta a 'yan kwanakin baya.
Da yake jawabi a wurin rabon kayayyakin, Aminu Dahiru,
babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kano kan daukar hoto, Aminu
Dahiru, ya jaddada kudirinsa na tallafawa ‘ya’yan jam’iyyar APC a dukkan
matakai, ta hanyar raba musu kayan tallafi ga dattawan jam’iyyar da kuma bayar
da tallafi ga mata da matasa domin su dogara da kansu.
Ya kara da cewa yanzu ne daidai lokaci ne da ya dace da
shi da sauran wadanda suka amfana da gwamnatin APC su koma gida domin tallafi jama’arsu,
wanda hakan zai taimaka masu a siyasar da zasu gudanar a nan gaba.
Aminu Dahiru ya yi alkawarin ci gaba da kyautata
alakarsa da mutane, inda ya kara da cewa zai ci gaba da mu’amala da mutane
kamar yadda ya saba ba tare da wani sauyi ba.
Comments
Post a Comment