Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya jinjinawa
shugaban shirin ciyar da daliban makarantun Firamare da Sakandare a jihar Kano Alhaji Uba Maga Yakasai, bisa irin kokarin da yake yi wajen bunkasa ciyarwar, ta
hanyar fito da sabbin tsare-tsaren kawo ci gaba a harkar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi jinjinar ne, lokacin da ya
kai ziyarar bazata Makarantar First Lady dake Mariri Hotoro.
Gwamna Abba Kabir, ya yabawa Alhaji Uba Maga kan yadda
yake aiki cikin gaskiya da rikon amana tare da jajircewa.
Ya kara da cewa, a dai-dai jihar Kano tana bukatar irinsu
Uba Maga don su tallafa mata wajen gyara barnar da gwamnatin baya tayi, yana
mai cewa Alhaji Uba Maga ne kadai zai iya gyara barnar da aka yi bangaren ciyar
da dalibai, tare da fito da sabbin hanyoyin da za a kara inganta harkar.
A cewar gwamna Abba Kabir. salo da tsarin shugabancin
Alhaji Uba Maga ya banbanta dana sauran, shiyasa tun daga lokacin da aka nada
shi ake ta samun ci gaba a fannin ciyar da dalibai.
A nasa jawabin shugaban shirin ciyar da dalibai na jihar
Kano Alhaji Uba Maga Yakasai ya godewa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan nada shi
wannan babban mukami.
Ya kara da cewa a lokacin da ya karbi aiki, ya tarar gwamnatin
baya ta lalata harkar gaba daya, har ta kai ga an dena ciyar da dalibai a
makarantu da dama, saboda irin badakaloli da aka samu.
A cewar Alhaji Uba Maga Yakasai abun da ya fara yi shi
ne, tsaftace tsarin tare da cusawa ma’aikata dabi’ar yin aiki cikin gaskiya da
rikon amana.
Wanda hakan ya taimaka kwarai da gaske wajen kawo
gagarumin sauyi cikin kankanin lokaci.
A karshe, Alhaji Uba Maga Yakasai ya bukaci gwamnan Kano
Injiya Abba Kabir Yusuf ya ci gaba da tallafa masa do samun gudanar da aikinsa
yadda ya kamata.
Comments
Post a Comment