Daga Abba Anwar
Da farkon farawa tukuna, na san mai karatu zai amince da ni idan na ce, tsohon Kwamishinan Kananan Hukumomi kuma tsohon dan takarar Mataimakin Gwamna a zaben 2023 a Kano, Murtala Sule Garo, ya na daga cikin mutanen da suke sahun gaba wajen ganin cewar jam'iyyar APC a Kano ta samu cikakken hadin kai da karfi tsakankanin 'yan jam'iyyar.
Ba wai maganar taimakon 'yan jam'iyya kawai nake ba, a'a ina fara magana ne kan yadda kauna da goyon bayan jam'iyyar yake a wajen jagororin APC a Kano.
Kowa ya san Garo ba mutum ne mai surutu ko hayaniya ko zantutttuka na ba gaira ba dalili ba. Shi kawai ya yarda da idan za a yi abu a yi ba sai an yi wani surutu ba. Abinda Turawa ke cewa "Action speaks louder than voice."
Ba ra'ayin wannan rubutun ba ne, ya soki wani dan jam'iyyar APC a Kano, daga kananun 'yan jam'iyya har zuwa ga jagorori ba.
Na yarda irin tarbiyyar da Garo ya samu a siyasa daga jagororin tafiyar siyasa, musamman shugaban jam'iyyar APC na kasa, wato Dr Abdullahi Umar Ganduje, ta sa za ka same shi mai hakurin da kau da kai ga abinda wasu ke ganin ya kamata ya dau fansa ta siyasa.
Ai kwanan nan lokacin da shugaban jam'iyya na kasa Baba Ganduje ya zo Kano yayin wani taro na masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC daga kananan hukumomi 44, Murtala Garo ya yi maganganu da yawa a wajen. Daga cikin abubuwan da ya fi bayar da karfi a wajen shine, ya yi kira da a yi tafiya daya dunkulalliya a jam'iyyance saboda kai wa ga gaci.
Cewa ya yi "Ya kamata a yi tafiya guda daya, uwa daya uba daya." Wannan din ya na gaya maka yadda jam'iyyar ke ransa. Ni akwai wanda ya taba gaya min, ba ma mutum daya ko biyu ba, cewar shi babbar matsalar Garo ita ce, ya fiye son jam'iyya da masifar biyayya ga shugabanni.
Na yi dariya na ce, lallai wani abu sai a siyasa, wai yin biyayya ga shugabanni da kuma tsananin son jam'iyya ya zama laifi wai. A lokacin wancan taron kowa ya ga yadda Garo ya yi korafin yadda a wasu yanayin a ke yin wariya tsakanin 'yan jam'iyya. Shi fa a wajen sa, komai ya kamata a yi shi a dunkule uwa daya uba daya.
Ni dai har yanzu ban gani ba da ido na ban kuma ji wani ya gaya min cewar, ga wani lokaci da Garo ya ce a je gidan rediyo ko wata kafar yada labarai ko a 'social media' a ci mutuncin wani dan jam'iyya ba balle ma a ce dan jam'iyyar ya na cikin jagorori.
Ni na san lokacin da tun lokacin da a ka hada shi takarar 2023 shi da daya dattijon, tsohon Mataimakin Gwamna, kuma tsohon dan takarar Gwamna, Dr Nasiru Yusuf Gawuna, da yawa wadanda abin bai musu dadi ba, sun samu Garo kan yadda ya kamata a yi tutsu. Amma Garo abinda kawai yake cewa shine, yadda Allah Ya tsara al'amari dole a yi hakuri a bi.
Na san sai da wani lokaci ya zo wanda sai da Garo ya fara nuna bacin ransa ga irin 'yan gutsuri tsoma din nan masu ganin cewa su fa idan ba shi ba, to sai dai a fasa kowa ya rasa. Kullum abinda yake fada shine, Allah Ya gama tsarinSa. Kodayaushe ya na nuna a kalli jam'iyyar kan ta a kuma kalli shugabanni a yi musu biyayya. Sannan a taimakawa 'yan jam'iyya na kasa su zauna lafiya.
Na yarda da Garo a irin maganganun da ya yi a wajen wancan taro cewar, abu mafi alheri da amfani da kuma adalci shine, in dai za a yi magana kan taimakon jam'iyya, to ya kamata a ce ba a ware kowa ba. Har ma shi da kansa ya kawo misalin Nasir Bala Ja'o'ji da kuma AA Zaura. Wannan shine adalci.
Daga baya bayan nan na san kungiyoyi da yawa da suke kewayen jagororin jam'iyya, duk kungiyar da ta je wajen sa, shawara daya yake ba su, a tsaya a yi aiki dan karfafa jam'iyya. Abinda yake gaya musu shine, ya kamata a manta da duk wani banbanci a sa jam'iyyar a gaba. To idan ba ka kira wannan son jam'iyya da biyayya ga jagorori ba, wane suna za ka ba irin wannan hobbasa dan Allah?
Bari in bayar da wani misali guda daya da zai kara haskawa mai karatu biyayyar Garo ga shugabanni. Lokacin zaben 2019 ai akwai wanda Garo ya fi sha'awar ya samu takarar Sanata ta Kano ta Arewa, wato tsohon Mataimakin Gwamna kuma tsohon Ministan Gidajen, Engineer Abdullahi T. Gwarzo.
Amma da Baba Ganduje ya nemi sulhunta tafiyar, ai daga baya sai kawai a ka ga Garo din dai ya kuma zama shine Babban Daraktan Kamfen na Sanata Barau Jibrin. Dan Allah idan ba biyayya ga shugabancin jagorori yaushe irin haka za ta faru?
Misali na karshe da zan bayar shine kan abinda ya shafi tsananin goyon baya da son da Garo yake yi wa Baba Ganduje a dukkan al'amuran Baban na siyasa da zamantakewar yau da kullum. Ina da yakinin cewa Garo ya na daya daga cikin kalilan na mutanen da ke kewaye da Baba Ganduje masu zama da Baban bisa amana.
Kullum zancensa shine, ta yaya Baba Ganduje zai samu nasara a siyasar sa. Ya sha gaya min cewar "Samun nasarar Baba Ganduje ita ce samun nasarar duk dan jam'iyyar APC a wannan jiha ta mu."
Kuma babban abinda yakewa kowa dadi shine, shi kansa Baba Gandujen ya gane haka ya kuma san hakan. Misali a kalli irin rawar da Garo ya yi a wannan ziyarar yan kwanaki da Baba Ganduje ya yi a jihar Kano satin da ya gabata.
Zan iya cewa, Murtala Garo, kamar yadda Turawa ke cewa shine "Alpha and Omega" a dukkan tsare-tsaren abubuwan da su ka gudana a wannan ziyara ta Baba Ganduje ya kawo Kano.
Wani babban abin alfaharin kowa shine, Baba Ganduje a wajen sa ba wani wanda yake shine danlele. Ya dauki kansa a matsayin uban kowa. Sai dai kamar yadda tsarin kowane magidanci yake a rayuwar mu ta yau da kullum, shi baban 'ya'ya ya fi kowa sanin wane dan ne ya fi kyautata masa da biyayya da neman albarka da cigaba da rufin asirin shi Baban yaran.
Fatanmu a kullum shine Allah Ya kara hada kan 'yan jam'iyya. Kanana da manya. Mabiya da jagorori.
Anwar shine tsohon Babban Sakataren Yada Labarai na tsohon Gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje,
4 ga watan Disamba, 2024
Comments
Post a Comment