Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya jinjinawa shugaban shirin ciyar da daliban makarantun Firamare da Sakandare a jihar Kano Alhaji Uba Maga Yakasai, bisa irin kokarin da yake yi wajen bunkasa ciyarwar, ta hanyar fito da sabbin tsare-tsaren kawo ci gaba a harkar. Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi jinjinar ne, lokacin da ya kai ziyarar bazata Makarantar First Lady dake Mariri Hotoro. Gwamna Abba Kabir, ya yabawa Alhaji Uba Maga kan yadda yake aiki cikin gaskiya da rikon amana tare da jajircewa. Ya kara da cewa, a dai-dai jihar Kano tana bukatar irinsu Uba Maga don su tallafa mata wajen gyara barnar da gwamnatin baya tayi, yana mai cewa Alhaji Uba Maga ne kadai zai iya gyara barnar da aka yi bangaren ciyar da dalibai, tare da fito da sabbin hanyoyin da za a kara inganta harkar. A cewar gwamna Abba Kabir. salo da tsarin shugabancin Alhaji Uba Maga ya banbanta dana sauran, shiyasa tun daga lokacin da aka nada shi ake ta samun ci gaba a fannin ciyar da dalibai. ...
Factual and verifiable Political News